Tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan ikirarin cewa ba zai binciki yadda aka kashe kudaden tsaro a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba. Shehu Sani ya bayyana hakan ne a cikin shirin Politics Today na Channels Television ranar Talata. […]
Shehu Sani ya soki Tinubu kan kin binciken kudaden tsaro da akayi a lokacin Buhari