Rundunar ‘yan sanda anan Kano ta sanarda kama wani matashi bisa zargin kitsa rikicin da ya ɓarke tsakanin ’yan daba na Kofar Mata da matasan Zango da ya faru kwanan nan. Matashin mai suna Kabiru Jamilu mai shekara 21, mazaunin rukunin gidaje na Zango Quarters an kamashi ne Unguwar Kofar Mata kusa da Asibitin kwararru […]