Mutane biyu sun rasa rayukansu a cikin wani hadarin mota da ya faru ranar Alhamis a kauyen Rumfa Biyu, cikin karamar hukumar Kafin Hausa, Jihar Jigawa. Hadarin ya faru akan Titin Dutse-Kafin Hausa. Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, Shi’isu Adam, ne ya tabbatar da hadarin a ranar Alhamis, inda ya ce: […]